Daga Hassan Y.A. Malik

Sojin Nijeriya, a yau Talata, sun sanar cewa sun tseratar da mutane 46 da mayakan Boko Haram ta yi garkuwa da su, a yayin da sojojin suka yi nasarar kwace, tare da rusa wani sansani ‘yan Boko Haram da ke can cikin tsakiyar dajin Sambisa, a kokarin dakarun na kakkabe ‘yan tawayen daga dajin.

A sanarwar ta sojin, wacce Kanal Onyeama Nwachukwu wanda shi ne mataimakin kakakin rundunar soji ta ‘Operation Lafiya Dole’ ya fitar jiya a Maiduguri, ya bayyana cewa rundunar Lafiya Dole ta kutsa can cikin dajin Sambisa, kuma ta yi nasarar ragargaza wani babban sansanin mayakan Boko Haram mai suna Sabilil Huda.

Rundunar ta yi nasarar fatattakar mayakan Boko Haram da dama, ta kuma rusa matsuganai a sansanin tare da kwato manyan makamai da dama.

Farmakin na rundunar Lafiya Dole na jiya Litinin ya karbo mata 19 da kananan yara 27, wanda wannan adadi ne ya bayar da mutane 46 da aka yi nasarar karbowa daga sansanin Sabil Huda.

LEAVE A REPLY