Al’umar garin Soro sun kaure da murna bisa shimfide babban masallacin garin Soro dake Karamar Hukumar Ganjuwa da sabuwar carpet ta zamani wanda mai girma Gwamna Muhammad Abdullahi Abubakar ya dauki nauyi. Da yake mika carpet din wa kwamitin masallacin Alh Yakubu Kafin Galadima, Chairman na Jamiyyar APC, Ganjuwa LGA a madadin sa, Yace Mai Girma Gwamna Yabada umarni a fara sallah cikin wannan masallaci ba tare da bata lokaci ba ganin watan ramadan yazo.
Dama dai Gwamnan ne ya dauki nauyin gyaran masallacin wanda ya kwashe shekara da shekaru a lalace ba a sallah a ciki. Shimfida carpet da mai girma Gwamna yayi a yau ya kawo karshen wannan aiki na gyaran masallacin.
Malamai da al’umar garin sun gudanar da addu’o’i na musamman ga mai girma Gwamna inda sukayi adduar Allah Ya kareshi, Ya masa jagora, Ya biya masa bukatunsa, Ya kuma bashi nasarar lashe zabe mai zuwa domin cigaba da zubawa al’umar Jihar Bauchi romon dimokradiyya.

LEAVE A REPLY