A gobe talata ne ake sa ran Shugaba Buhari zai ziyarci birnin lafiya ta jihar Nassarawa a daidai lokacin da rikici yayi tsamari tsakanin manoma da makiyaya a jihar. Al’umma da dama na fatan wannan ziyara ta sanya kawo karshen wannan rikici.

Mai baiwa Gwamnan jihar Nassarawa Umar Tanko Al-Makura shawara na musamman kan harkokin dalibai da matasa da kuma kungiyoyi masu zaman kansu, Samuel Akala ya bayyana cewar wannan ziyara ta Shugaba Buhari a jihar zata kawo alheri ta fuskar zaman lafiya.

“Duk da cewar wannan ziyarar ba zai kawo ta bane domin wannan rikici da ya yawaita a jihar, amma dai muna fatan wannan ziyara ta sanya kawo karshen wannan rikici da zarar Shugaban ya sanya kafarsa a jihar Nassarawa”

“Muna da yakinin cewar, Shugaba Buhari yana da masaniyar abubuwan da ke faruwa a jihar Nassarawa na wannan rikici da yaki ci yaki cinyewa tsakanin manoma da makiyaya”

“Ni da sauran jami’an Gwamnati mun kai ziyara sansanin da aka tsugunar da wanda wannan rikici ya rutsa da su, sun bayyana min cewar suna fatan zuwan Shugaba Buhari ya zauna da dukkan bangarorin guda biyu domin samun maslaha”

Fitaccen dan kasuwa a lafiya, Abubakar Sandaji, ya bayyana gamsuwarsa da wannan ziyara ta Shugaba Buhari, inda yace, yana fatan wannan ziyara tasa ta kawo karshen zubar da jini tsakanin manoma da makiyaya.

“Yana daga cikin ingancin Shugaba na gari, shi ne yayi kokarin sasanta al’ummarsa da suke rikici da juna, doin su zauna lafiya cikin aminci”

Shugaban al’ummar Tibi nna jihar Nassarawa, Bonifece Ifer yace tsammanin al’ummar Tibi a yayin wannan ziyara ta Shugaba Buhari ita ce ya yi batun da zai magance wannan matsala ta manoma da makiyaya.

Shugaban kungiyar Miyatti Allah ta al’ummar Fulani, reshen jihar Nassarawa, Mohammed Hussaini, ya bayyana jin dadinsa da wannan ziyara da Shugaban zai kai jihar, yace duk da wannan ziyara ta Shugaba Buhari ba tada alaka da batun rikicin da yake faruwa a jihar, amma dai suna fatan ziyarar ta kawo karshen rikicin.

“Shugaba Buhari mutum ne mai son zaman lafiya. Duk da cewar zai zo jihar Nassarawa ne domin kaddamar da wasu ayyuka, muna da yakinin cewar zai yi abinda ya dace wajen sasanta al’ummar da ke rikici da juna tsakanin manoma da makiyaya”

“Shugaba Buhari jakada ne na samar da zaman lafiya”

NAN

LEAVE A REPLY