Ministan harkokin cikin gida Abdulrahman Dambazau

Biyo bayan tattaunawa da ake ta yi a tsakanin Gwamnonin kasar nan, domin tattauna mafitar rikicin da ake fama da shi tsakanin Manoma da Makiyaya, ministan harkokin cikin gida, Abdulrahman Dambazau a ranar talata ya zayyana hanyoyi biyu da suke janyo aukuwar rikici a lokacin da yayi wani taro na gaggawa da manyan jami’an tsaro a Abuja.

A lokacin da yake zantawa da manema labarai, Dambazau ya bayyana cewar “Daya daga cikin muhimman batutuwan da muka tattauna a jawabin bayan taronmu shi ne, batun yadda kananan makamai suke zarya a hannu bangarorin biyu da kumata’amali da kayan maye”

“Mun yi magana akan cewar wadannan batutuwa guda biyu na kayan maye da kuma bazuwar kananan makamai na daga cikin dalilin yawan samun rikicin da ake yi”

“Idan babu kananan makamai da kwayoyi, da yawan wadannan rikice rikice ba za’a same su ba a wannan kasa tsakanin bangarorin makiyaya na Fulani da kuma na Manoma”

” A sabida a samu mafita, na kirawo taron masu ruwa da tsaki akan harkar tsaro, domin mu duba hanyoyin d zamu iya bi na masalaha domin karshen wannan tashin tashina”

Dambazau ya habarto wani kwamitin majalisar dinkin duniya kan batun dakile bazuwar kananan makamai a hannu jama’a, inda rahotanni suka ce, akalla akwai sama da kananan makamai miliyan 500 a yankin yammacin Afurka, a cikin wadannan akalla akwai miliyan 350 a Najeriya, kamar misalin kashi 70 kenan suna kasarnan.

Yace, an taba kama wani katon sunduki cike fal da miyagun makamai, wanda aka shigo da shi daga Arewacin Afurka, kudu da hamada sahara, musamman kasar Libiya zuwa wannan kasa.

“Yanayin da ake ciki, yayi matukar muni kwarai da gaske, ayyukan ta’addanci na karuwa a yankin Arewa maso gabas, sabida yadda wadannan kananan makamai din ke bazuwa a tsakanin ‘yan ta’adda”

“Haka nan batun yake,kan batun mutanan yankin Neja Dalta, suma haka nan,aka yada kananan makamai tsakaninsu”

“Abu ne da ya zamar mana dole, mu magance ko mu dakile yaduwar wadannan makamai, domin smar da dawwamammen zaman lafiya a wannan kasa, wannan kuma babban kalubale ne musamman kan iyakokin kasarnan, dole ne hukumar dake kula da shige da fice su sanya ido sosai tare da hukumar kwastan ta kasa”

Ya bayyana cewar batun Sace mutane ayi garkuwa da su domin neman kudin fansa, da kwace da zari ruga da fashi da makami, da masu kungiyar asiri da rikicin kabilanci da na addini da fadan manoma da makiyaya, duk yana da alaka ta kai tsaye da kayan maye da bazuwar kananan makamai.

A yayin wannan zaman dai akwai wakilan hukumar Kwastan ta kasa da hukumar hana fasakwauri ta kasa da jami’an tsaron farin kaya na DSS da kuma hukumar leken asiri ta kasa NIA.

Sauran sune, NSDC da NDLEA da da sauran dangin jami’an tsaro.

LEAVE A REPLY