Sanata Mohammed Bello

Daya daga cikin jigo a jam’iyyar PDP a jihar Kano, Mohammed Bello ya bayyana cewar rikicin da ake samu tsakanin Kwankwaso da Ganduje babbar riba ce ga jam’iyyar PDP a zaben 2019.

Mohammed Bello, wanda tsohon Sanata ne da ya wakilci Kano ta tsakaiya a majalisar Dattawa karkashin rusasshiyar jam’iyyar ANPP, yace babu wanda zai amfana da wannan rikicci na Kwankwaso da Ganduje kamar PDP.

“Wannan rikici dama ce mai kyau ga jam’iyyar PDP, domin samun damar kwace kujerar Gwamnan Kano. A ko da yaushe idan aka samu irin wannan rikici idan jam’iyyar adawa ta yi abinda ya dace tana tsintar dami ne a kale” A cewar Mohammed Bello lokacin da yake tattaunawa da jaridar Daily Trust.”

“Ba batu ne na sabuwar jam’iyya ba, batu ne na jam’iyyar da take da tsari a dukkan mazabu da kananan hukumomi, dan haka PDP ta kwace wannan Gwamnati ba wani bau bane mai wahala idan anyi shirin da ya dace, Muna da Malam Ibrahim Shekarau da Amainu Wali, zamu iya mai da wannan sabani ya zama alheri garemu”

Mohammed Bello wanda ya taba rike mukamin Kwamishinan gona da na ma’aikatar Muhalli a jihar Kano, zamanin Gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau, ya cigaba da cewar, duk da PDP na da nata matsalolin amma hakan ba zai hana mana amfana da wannan rikici ba.

“Misali, da yawan ‘yan Najeriya sun tsammaci abubuwa da yawa a jam’iyya mai mulki ta APC, amma kuma babu wani canji da aka gani a kasa”

“Mutane da dama na akorafin basa iya samun cin abinci sau uku sabida tsananin rayuwa da suke ciki. Ana samun mutane na haura gidajen mutane suna satar abinci, wannan kuwa ba abu bane mai sauki faruwar irin haka, a sabida haka ya zama wajibi a canza wannan Gwamnatin” A cewarsa.

Haka kuma, kwana kwanannan muka ji Shugaban kasa ya nada Bola Ahmedd Tinubu ya sasanta irin rikita rikitar da ake fama da ita a jam’iyya mai mulki, kaga kuwa wannan alama ce ta samun baraka, kuma nasara a garemu.

 

LEAVE A REPLY