Daga Hassan Y.A. Malik

Akalla mutune biyar ne suka rasa rayukansu a yayin wata karawar rikicin kabilanci tsakanin wata kabila da ke yankin karamar hukumar Yakurr da wata kabilar da ke a karamar hukumar Obubra duk a cikin jihar Cross River.

Lamarin dai ya faru ne a safiyar jiya Juma’a dalilin da ya jawo asarar dukiya mai yawa da suka hada da gidaje da saura kadarori na miliyoyin Naira.

Wani direban bas da ya bayyana sunansa sa Michael Ojong ya bayyana cewa sakamakon tsanani da fadan ya yi a jiya sai da ya juya da fasinjojinsa suka koma Calabar.

Da aka tuntubi kwamishinan ‘yan sandan jihar. Muhammed Inuwa Hafiz, ya bayyana cewa tuni ‘yan sanda sun shawo kan al’amarin.

A tabakin kwamishinan, “Wannan lamari ne da ya kan faru daga lokaci zuwa lokaci tsakanin kabilun biyu, hakan ya sanya a kodayaushe muke ankare.

“Muna samun rahoton an fara rikicin sai muka tura jami’anmu don su gaggauta kwantar da rikicin. Zuwa daren jiya dai ban samu rahoton rasa rai ba, sai dai an kona gidaje da dama.”

LEAVE A REPLY