A jiya Talata ne rikici ya barke tsakani Fulani makiyaya da manoma a jahar Ebonyi, lamarin da ya haddasa jikkatar mutane 4.

Yayin da Fulani 3 suka samu raunika a kawunan su, daya daga cikin manoman ya samu yanka a gurare daban daban a sassan jikin shi.

Yanzu haka manomin na samun kulawa a asibitin gwamnatin tarayya da ke Abakaliki, babban birnin jahar, yayin da Fulanin ke asibitin Awgu da ke jahar Enugu.

Tuni dai mazauna yankin suka tsere daga gidajensu gudun kar Fulanin su kai masu harin ramuwar gayya.

Rahotanni sun bayyana yadda Fulani daga garin Mpu a jahar Enugu suka afkawa wata gona a yankin Akaeze da ke jahar Ebonyi inda suka yi kaca-kaca da gonar, lamarin da ya hassala manomin har ta gai ga ya yi magana, inda daga nan ne rikicin ya fara bayan da fulanin suka afkawa manomin da sara da suka.

Tuni gwamnan jahar, David Umahi, ya haramta kiwo a karamar hukumar har sai an kammala bincike game da batun tare da kafa kwamiti mai kunshe da mutane 10.

Gwamnan ya kuma kira taro da sarakunan gargajiyan jahar da shugabannin fulani makiyaya, da shugabannin kananan hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki domin shawo kan lamarin.

Umahi ya ce duk manomin da ya kashe shanun makiyaya zai tafi kurkuku haka zalika duk makiyayin da ya lalata gonar manomi zai tafi kurkuku shi ma.

Sai dai ya ce dole kowane Bafulatanin da zai shiga jahar ya bi ka’idar bi ta kan titina ba ta cikin jeji ba.

LEAVE A REPLY