Gwamnan jihar Binuwai Samuel Ortom

Daga Hassan Y.A. Malik

Akalla gidaje 54 ne suka ci wuta, dalilin da ya sanya mutane da dama suka rasa matsugunansu a wani rikicin tsakanin al’ummar garin Mbamar da ta garin Ugambe duka a karamar hukumar Koshinsha ta jihar Binuwai.

Majiyarmu ta gani cewa abinda ya haddasa rikicin ba komai bane face wani fili da ke a kan iyakar garuruwan biyu da al’ummar garuruwan ke jayayya akan mallakarsa.

Daily Nigerian ta gano cewa rikicin ya fara ne tun a lokaci mai tsawo, amma ya ta’azara ne bayan da matasan garin Ugambe suka kai hari akan wani dan garin Mbamar kuma suka gididdiba shi da adda.

Kakakin ‘yan sandan jihar Binuwai, ASP Moses Yamu ya tabbatar da faruwar al’amarin inda ya kara da cewa tuni har ‘yan sanda sun cafke mutane 22 da ta ke zargi da hannu a farauwar rikicin a garuruwa biyun.

Kakakin ya tabbatar mana da cewa hukumar ‘yan sanda za ta gurfanar da mutanen a gaban kotu da zarar ta kammala bincikenta.

LEAVE A REPLY