Daga Hassan AbdulMalik

A yayin da rikakken mai garkuwa da mutanen nan, Evans Chukwudumeme Onwaumadike ke fuskantar shari’a a kotu, ‘yan sanda sun sake samun nasarar cafke wani rikakken mai garkuwa da mutane da sana’ar sayar da motocin sata a jahar Niger mai suna Isah Mai Turare.

Wannan dai shine karo na 8 da aka kama Mai turare a cikin shekaru 29 tun da ya fara sana’ar garkuwa da mutane kuma ya je kurkurku har sau 7.

Yayin da manema labarai ke Magana da shi, Mai Turare ya shaida masu cewa shi dama ya gaji da rayuwar kuma tuni ya roki ubangiji ya dauki ran shi a wannan shekara.

Mai Turare dai dan asalin karamar hukumar Paikoro ne a jahar Niger, ya na da shekaru 61 a duniya, mata 3 da yaya 29. Ya shahara a sana’ar garkuwa da mutane da sayarda motocin sata a cikin jahohi Niger, Kogi, kaduna da Kano.

A cewar shi, a cikin shekaru 4 kacal, shi da yaran shi sun samu sama da Naira miliyan 720 na kudaden fansa.

Ya ce ya bar sana’ar satar mutane a shekarar 2013, inda ya maida hankalin shi a sayar da motocin sata, amma shekaru 3 da suka gabata, matsin rayuwa ya sanya shi komawa.

A baya dai, a duk lokacin da Mai Turare ya je kurkuku kuma ya fito, duk da cewa wa’adin da aka yanke masa bai cika ba, ya kan kira jami’an tsaro da Gadara ya shaida masu cewa ya fito kuma zai ci gaba da sana’ar sa kamar yadda ya saba.

A cewar shi, “Ban yi da na sanin abunda na yi ba a wadannan shekaru 29, amma yanzu lokacin mutuwa ya yi kuma abunda na ke jira kenan. Na fadawa ubangiji ina son na mutu a wannan shekara”

Rahotanni daga jaridar Sunday Sun sun bayyana cewa Mai Turare na da gidaje sama da 35 a Minna, Kaduna da Kano.

LEAVE A REPLY