Rikakken mai garkuwa da mutane, Evans

Daga Hassan Y.A. Malik

Rikakken mai garkuwa da mutanen nan da ya dade da shiga hannun hukuma, Evans ya yi ta sharara kuka a yayin da ya bayyana a gaban kotu a yau Litinin.

Evans ya fadawa kotun da ke zama a Igboshe a jahar Lagos cewa ya na matukar shan azaba a gidan kurkukun kirikiri inda ya ke ajiye, hasali ma ko samun abinci ba ya yi.

Jaridar Daily Post ta rahoto yadda aka samu turjiya a harabar kotun lokacin da Evan ya ki sauka daga motar ‘yan sanda har sai da Alkali Adedayo Akintoye ya ba da umarnin a shigo da shi cikin kotu da karfi.

“Me na yi wa mutanen da suke ta duka na? Babu abinci. An tsare ni a wani waje guda tun ranar 30 ga watan Agusta. Me ya sa suka dauki lamari na ba tare da muhimmanci ba?

“A bar ni na fuskanci doka a raye, me ya sa ku ke son kashe ni?,” inji Evans yayin da yake zubar da hawaye.

 

LEAVE A REPLY