Joji Abdul Kafarati

Babban CifJojin Najeriya, Walter Onnoghen, a ranar Talata a babban birnin tarayya Abuja ya jagoranci rantsar da Abdul Kafarati a matsayin sabon Jojin babbar kotun tarayya.

Bayan da sabon jojin babbar kotun tarayyar ya sha rantsuwar kama aiki, Babban jojin tarayya Walter, ya hore shi da ya rike aikinsa hannu bibiyu tare da lura da tanade tanaden kundin tsarin mulkin shekarar 1999 a ko yaushe.

“Ba ni da bukatar nai maka nasiha domin ka sha rantsuwar kama aiki, domin wannan abu ne da ka shanshi a gaba daya rayuwarka ta aiki, sai dai kawai nai maka fatan samun jagoranci abin misali”

 

LEAVE A REPLY