Shugaban Hukumar zabe ta kasa, Farfesa Mahmoud Yakubu

Hukumar zabe ta kasa INEC ta bayyana cewar, ba zata sauya ainihin ranakun zaben da ta sanya ba tun da farko. INEC ta bayyana hakan ne a ranar Talata bayan da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi fatali da bukatar sake fasalin zabe kamar yadda majalisun tarayya suka zartar.

Darakta mai lura da sashin ilimantarwa da da wayar da kai, Oluwole Uzzi, shi ne ya bayyana hakan inda yace “Zamu yi aiki da ainihin ranakun zaben da muka fitar tun da fari”

A lokacin da aka tambayeshi cewar, ko majalisun dokoki na tarayya suna da ikon sauya ranakun zabe a Najeriya, ya ce; “Wannan kuma batu ne da lauyoyi zasu yi fashin baki akansa”

Idan ba’a manta ba, tuni hukumar zabe ta kasa ta fitar da ranakun 16 ga watan Fabrairu a matsayin ranar da za’a yi zaben Shugaban kasa da ‘yan majalisun tarayya, da kuma ranar 2 ga watan Maris, a matsayin ranarda za’a yi zaben Gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi.

Sai dai kuma, majalisun dokoki na tarayya sun aiwatar da gyaran fuska ga dokokin zaben, inda suka raba zaben Shugaban kasa da na ‘yan majalisun dokoki na tarayya.

A ranar Talata, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikewa da majalisun dokoki na tarayya wasikar kin amincewarsa da batun sake sauya fasalin zaben na 2019.

LEAVE A REPLY