Ustaz Mustapha Umar Hassan
Anyi kira ga mawadata da su tallafawa marasa karfi a wannan watan mai alfarma na Ramadan domin samun gwaggwaban lada a wajen Allah, Ustaz Mustapha Umar Hassan ne yayi wannan kiran ga al’umma, inda ya ja hankali akan falalar taimakon marasa karfi kamar haka:
“Hakika watan Ramadan wata ne na taimako da tausayin wanda da ba su da shi, wata ne da Allah yake ninka aiyukan bayi, duk wanda ya ciyar da wanda ba shi da shi Allah zai bashi lada mai tsoka.
Annabi ‘SAW’ yace duk wanda ya ciyar da mai azumi Allah zai bashi lada kwatankwacin wanda yayi azumin, ba tare da an tauyewa wanda yayi azumin ladansa ba.
Sahabbai sun kasance suna nemo talakawa su zo su sha ruwa atare da su, idan suka gama su roke su da su sake dawowa gobe su sha ruwan dan kwadayin lada.
Muna da masu kudi da masu mulki, da ace sahabbai ne suke da irin dukiyar da muke da ita da ba asamu mutumin da zai rasa abinda zaiyi sahur ba ko Buda baki ba.
Masu kudinmu basu da zuciyar kyauta sai zuciyar alfahari, masu mulkin mu basu da zuciyar tausayi sai zuciyar mulki, su samu mulki ta kowani hali su dai ganmu akasansu.
Duk mai kudin da ya mutu bashi da zuciyar taimako, ko mai mulkin da ya mutu bashi da zuciyar adalci sai yafi talaka zama abin tausayi a lahira.
Annabi ‘SAW’ shi yafi kowa tausayi da taimako, yace duk wanda akebi bashi bashi da abin biya ya zo ni zan biya masa.
Ya Allah ka azurtamu da abinda zamu taimaka ma wanda ba shi da shi, duk dukiyar da bata taimako ba Ya Allah karabamu da Ita.”

LEAVE A REPLY