Badaru Abubakar

Gwamnain jihar Jigawa ta amince da rage awanni biyu a aikin Gwamnati a jihar domin baiwa ma’aikata damar komawa gidajensu su yi wasu aikace aikace kafin lokacin buda baki tare da iyalansu.

Jami’in hulda da jama’a na ofishin Shugaban ma’aikatan Gwamnatin jihar Ismail Ibrahim ne ya bayyana hakan ga manema labarai a birnin Dutse a ranar Asabar.

Ya bayyana cewar daga yanzu ma’aikata zasu dinga zuwa aiki ne da misalin karfe 9 na safe kuma su tashi da karfe 3 na rana, mai makon karfe 8 da ake shiga a tashi karfe  na yamma daga ranakun Litinin zuwa Alhamis.

 

LEAVE A REPLY