Shugaban Kungiyar CISLAC, Auwal Musa Rafsanjani

Shugaban kungiyar CISLAC mai sanya idanu kan harkokin Majalisa, Auwal Musa Rafsanjani ya caccaki salon Gwamnatin Buhari na yaki da cin hanci da rashawa a najeriya. Yayi bayani yadda ake take dokokin kasa, tare da yin wancakali da rahotannin da aka gabatarwa Gwamnati kan batun cin hanci.

Rafsanjani ya bayyana hakan ne a zantawarsa da sashin hausa na BBC a ranar talata. Ya zargi jami’an Gwamnati da yin facaka da dukiyar Gwamnati amma an kauda kai daga garesu. Ya kuma kara da cewar, akwai rahoton da aka gabatarwa da shugaban kasa kan batun almundahana da Sakataren Gwamnati BD Lawal yayi amma shugaban yayi shiru bai ce komai ba.

Ya kara da cewar, aa matsayin kungiyarsu na masu sanya ido kan batun cinhanci da rashawa, baya jin dadi yadda Gwamnatin Buhari ke bin irin salon Mukin Gwamnatin Jonathan da ta gabata, yace mutane da yawa sunyi laifi memakon a koresu sai a yaba musu.

Ya bayar da misali kan Daraktan NIA da batun Ministan man-fetur da Kachikwu da Mai-Kanti Baru. Yace abubuwa ne da ya kamata ace shugaban ya dauki hukunci akansu, amma an bar mutane suna facaka suna cin karensu babu babbaka.

Me zaku ce kan wannan batun da Rafsanjani yayi?

LEAVE A REPLY