Hoton 'yan matan Makarantar Dapchi wanda The Nation ta dauka

 

Hassan Y.A. Malik

Rahotanni sun bayyana cewa rabin ‘yan matan makarantar gwamnati ta Dapchi da ‘yan Boko Haram suka sace a makon da ya gabata an ketara da su jamhuriyyar Nijar ta wani karamin rafi.

Ko a jiya sai da jaridar Daily Trust ta bayyana wata majiya sahihiya da tabbatar da cewa an raba ‘yan matan gida biyu; rabi na farko na adain’yan matan na nan a wata maboya a cikin arewacin jihar Borno, inda daya rabin kuma aka tsallaka da su zuwa wani kauye cikin kasar Nijar.

Haka kuma, majiyar ta bayyana cewa, bangaren Abu Mu’ab Albarnawi na kungiyar Boko Haram wanda ke da alaka da kungiyar ISIS ne suka sace ‘yan matan na Dapchi.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, kaso 1 bisa 2 na ‘yan matan na yankin Tumbun Gini cikin karamar hukumar Abadam da ke da helikwata a garin Malam Fatori, jihar Borno.

Daya rabin kuma an tsallaka da su ne ta wani karamin tafki da ke garin Duro, kan iyakar Nijeriya da Nijar.

 

LEAVE A REPLY