Wani sashi na Baburan da aka rabawa Kansiloli a jihar Zamfara

Shugaban karamar hukumar mulkin Gusau ta jihar Zamfara Ibrahim Umar Tanko ya gwangwaje kansilolin majalisar zartarwasa da sabbin baburan hawa.

Mutane da dama suna yabawa shugaban karamar hukumar bisa wannan namijin kokari da yayi na gwangwaje sabbin kansilolin da ababen hawa, yayin da wasu ke ganin baikensa kan hakan.

Abdulmalik Saidu Gusau wani mai sayar da burodi a tsahar baga Gusau ya bayyanawa DAILY NIGERIAN HAUSA cewar wannan ba wani abin yabawa ba ne dan an baiwa kansiloli babura.

A cewarsa, cin fuska ne don an baiwa kansila babur a yi terere da shi.

LEAVE A REPLY