Shugaba Muhammadu Buhari

Mai magana da yawun fadar Shugaban kasa Mallam Garba Shehu ya mayarwa da jam’iyyar PDP martani kan zargin da jam’iyyar ta yi na sayan masu zabe da aka yi a yayin zaben cike gurbi da aka gudanar a jihohin Kogi da Katsina da kuma Bauchi wanda jam’iyyar APC mai mulki ta lashe.

Da yake shaidawa manema labarai a fadar Shugaban kasa, Garba Shehu ya bayyana cewar, yin amfani da kudi a lokacin zabe babban laifi ne, a dan haka ya bayyana cewarduk wani wanda yake da hujjar cewar jam’iyyar APC ta yi amfani da kudi domin sayen masu zabe yana iya kai abin gaba.

“Baiwa masu zabe kudade domin su zabi jam’iyya wannan abu ne da ya sabawa dokar kasa, kuma muna fatan duk wani wanda yake da hujjar cewar an yi amfani da kudi wajen sayen masu zabe yana iya mika abin ga sashin shar’ah domin hukunta duk wanda aka samu da laifi”

“Sam bai kamata ba ga jam’iyyun adawa sun dinga yin abubuwan da basu dace ba, dan kawai suna da matsala da sakamakon zabe, jam;iyya ta zama tamkar kungiyar miyagun mutane, wannan bai kamaci ‘yan adawa baa, duk wanda yake da hujjar an yi masa rashin gaskiya, yasan hanyar kotu kuma yana iya zuwa yakai koke”

“Gwamnan jihar Anambara Willi Obiano yaci zabe, Shugaban kasa yataya shi murna, duk da cewar jam’iyar SHugaba Buhari ta zo na biyu a zaben, to bai dace ba ‘yan adawa su mayar  da komai fada basa yin abu akan tsari”

LEAVE A REPLY