Gwamnan jihar Kaduna, Nasiru el-Rufai

Dan takarar Shugabancin karamarhukumar Jaba na jam’iyyar PDP, Phiip Gwada shi ne ya lashe zaben Shugabancin karamar hukumar da aka sake yi a wannan makon.

Baturen zaben, Grace Doyaro, ita ceta sanar da sakamakon zaben a garin Kwoi na karamar hukumar a ranar Alhamis, shi dai Gwada ya lashe zaben da kuri’u 17,967 inda ya kayar da abokin karawarsa Benjamin Jok na jam’iyyar APC da kuri’u 7,401.

Baturiyar zaben Doyaro ta bayyana cewar an udanar da zaben cikin kyakkyawan yanayi, tare da gudanar da shi cikin gaskiya da aminci.

LEAVE A REPLY