Matar tshohon shugaban kasa Goodluck Joathan
Mai ɗakin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, Patience Jonathan, ta zargi hukumar yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC da cewar tana yi mata bita da ƙulli. Sannan kuma ta roki shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya shiga tsakaninta da hukumar ta EFCC.
 
Patience din ta bayyana haka ne, ranar litinin a Abuja, ta hannun mai magana da yawunta Mista Belema Meshack-Hart.
Ta ce shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu, “yana shirya min muguwar kitimururar da zata lalata min rayuwa”.
 
Ta ci gaba da cewa, “abinda Magu yake yi sam bai dace ba, domin karara bita da kulli ne akaina, hakan kuma ba komai bane, face zubar da kimar hukumar tasa a idon duniya”.
 
Bayan haka kuma, matar tsohon shugaban ƙasar, ta zargi Magu da shirya bayanan da ba su da tushe balle makama akanta, ta ce galibin abinda ake yadawa akanta ƙarya ake yi kanta.
Tun fiye da shekara uku, hukumar EFCC ta kafa min ƙahon zuƙa, ana son lallai sai an kama ni da laifin da za’a ci zarafina, a cewar Patience Jonathan.
 
Hukumar ta EFCC dai na yiwa matar tsohon shugaban ƙasar, zarge zarge da su ka shafi almundahana da kuɗaɗe masu dumbin yawa da sunan gidauniyar da ta kafa, kamar yadda bisa ga al’ada matan shugabanni kan kafa wasu kungiyoyi da zasu dinga aiki ƙarƙashinsu.
 
Duk wani yunƙuri na yin magana da kakakin hukumar ta EFCC Mista Wilson Uwujaren, ya ci tura.
Sai dai wani ma’aikacin hukumar da bai yadda a ambaci sunansa ba, ya musanta cewar hukumar na yi wa matar tsohon shugaban kasa bita da kulli ne.
 
Ya ƙara da cewar, hukumar bata yiwa matar wani abu mai kama da bita da kulli, a cewarsa, abinda suke yi bincike ne a kanta, kamar yadda hukumar ke bincikar mutane da dama.
 
Ya cigaba da cewar duk wanda ya san yana da gaskiya kada ya tsoraci komai, zasu gudanar da bincike, kuma su mika duk wanda su ke zargi zuwa kotu don fuskantar ta. Sai dai duk mai gaskiya to gaskiyarsa zata kubutar da shi.
 
Me zaku ce akan satoka-sa-katsin da ake yi tsakanin matar tsohonshugaban kasa da hukumar binciken yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati ta EFCC?
 
 

LEAVE A REPLY