Sabon Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole

Sabon zababben Shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole wanda ya sha rantsuwar kama aiki a ranar Lahadi a matsayin Shugaban jam’iyyar na kasa, ya bayyana cewar yana gaggawar shiga ofis domin tunkarar matsalolin da suke damun jam’iyyar.

Oshiomhole wanda shi ne ya ci nasarar zama sabon Shugaban jam’iyyar APC na kasa biyo bayan babban taron jam’iyyar na kasa da ya gudana a babban birnin tarayya Abuja, ya bayyana a yayin da yake jawabin amincewa da zabensa a matsayin Shugaban jam’iyyar na kasa a Eagle Square, inda aka yi babban taron jam’iyyar.

Ya bayyana cewar yana kira ga tsaffin ‘yan sabuwar PDP dake cikin jam’iyyar kuma suke jin cewar ba’a yi musu daidai ba, da su yi hakuri su mayar da wukarsu cikin kube, su hada kai da su domin ciyarda jam’iyyar gaba da kuma ciyar da Najeriya gaba.

Adams Oshiomhole dai ya zama sabon Shugaban jam’iyyar ne bayan da dukkan masu neman mukamin Shugabancin jam’iyyar na kasa suka janye masa, inda ya ci zaben babu hamayya.

LEAVE A REPLY