Tsohon kakakin jam’iyyar PDP na kasa Chif Olisa Metuh ya yanke jiki ya fadi a kotu a ranar Litinin din nan da aka sake kiransa a kotun domin cigaba da fuskantar Shariar da hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta gurfanar da shi.

Hukumar EFCC na tuhumar Metuh ne akan zarginsa da karbar kudaden da suka kai naira miliyan 400 daga ofishin mai baiwa Shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro Sambo Dasuki a lokacin Gwamnatin PDP da ta shude.

Lamarin dai ya faru ne ranar Litinin da misalin karfe 9 na safe, inda aka shigo da Olisa Metuh a kotun domin cigaba da saurarn karar da ake yi masa, inda nan take ya yanke jikin ya zube a kasa.

Haka kuma, mai shariah Okon Abang yaki amincewa da batun baiwa Metuh damar zuwa asibiti neman magani, inda kusan ko yaushe ana kaishi kotu ne a nannade da bandeji kuma akan gadon daukar marasa lafiya.

LEAVE A REPLY