Olisa Metuh

Tsohon mai magana da yawun jam’iyyar PDP, Olia Metuh ya bayyana gaban kotu kan gadon asibiti, kamar yadda babbar kotun daukaka kara dake Abuja ta bayar da umarnin dole ya bayyana a gabanta ko a wanne irin hali yake ciki.

Mai shariah Okon Abang a wani hukunci da yayi a ranar 25 ga watan Janairun da ya gabata, ya ki amince da takardun asibiti da suka nuna cewar Olisa Metuh yana fama da rashin lafiya, wanda lauyansa ya gabatarwa da kotun.

A madadin hakan, Mai shariah ya umarci lallai Olisa Metuh ya bayyana a gabansa ko da kuwa za’a kawo shi ranga ranga, domin duba yuwuwar bayarda shiBeli.

Domin cika wannan umarni, lauyan Metuh ya sanya an kawo wanda yake karewa gaban kotun a motar daukar marasa lafiya mallakar babban asibitin kasa dake Abuja, kan gadon asibiti.

Bayan da aka iso harabar kotun da Olisa Metuh cikin motar daukar marasa lafiya, an fito da shi daga cikin motar kan wani gadon asibiti inda aka wuce da shi cikin kotun domin sauraren Alkali.

An lullube Olisa Metuh a da farin kyalle ta yadda ba’a ganin komai na jikinsa sai kansa kawai, domin bashi damar yin nufashi. Akwai bandeji shake da wuyansa da kuma kansa.

Kotu dai na yiwa Metuh da kamfaninsa na Destra Investment Limited shariah kan zargin cin hanci da kuma zambar kudade masu dumbin yawa.

Lokacin da aka fara zaman Kotun, Lauyan da yake kare Metuh, Onyechi Ikpeazu SAN ya shaidawa kotun cewar wanda yake karewa ya bayyana a gaban kotu bisa yadda kotu ta umarci lallai sai an zo da shi a kowanne hali yake ciki. Amma ba zai iya komai ba sabida yadda yake fama da jikinsa.

A yayin da ake fito da Metuh daga cikin motar daukar marasa lafiya.

Image result for Metuh attends court on stretcher

Likitoci na tura Metuh akan gadon Asibiti

Image result for Metuh attends court on stretcher

Abokan Metuh da iyalansa na taimakawa wajen shigar da shi cikin Kotu

Image result for Metuh attends court on stretcher

 

LEAVE A REPLY