Tsohon Shugaban kasa Olushegun Obasanjo

A daidai lokacin damanya manyan mutane suke tururuwar zuwa Jos babban birnin jihar Filato domin jajantawa Gwamnati da al’ummar jihar kan abinda ya faru na sarar rayukan sama da mutum 200 da aka yi a wannan makon.

Tsohon SHugaban kasa Olushegun Obasanjo yayi kira ga Gwamnati da ta dauki dukkan matakan da suka dace cikin gaggawa domin kawo karshen zubda jini a Najeriya, domin samun zaman lafiya mai dorewa.

A cewar tsohon Shugaban, matsalar da take damun al’umma, to al’umma ne suke da ikon warware ta, a saboda haka dole ne Najeriya ta nemo hanyoyi sahihai na warware rikita rikitarda ake fama da ita a Najeriyana kashe mutane babu ji babu gani.

Obasanjo ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kaiwa Gwamnan Filato Simon Lalong ziyarar jaje da kuma ta’aziyar mutanan da suka rasu a Jos babban birnin jihar sakamakon wannan rikici a jihar.

Obasanjo ya mika sakon ta’aziyarsa da na iyalansa, inda kuma ya nemi da Gwamnatin jihar ta matsa kaimi wajen baiwa rayuwa da dukiyoyin al’umma kariya a dukkan fadin jihar baki daya.

“ABin takaici ne kwarai da gaske yadda irin wadannan kashe kashe suke aukuwa a garuruwan kasarnan, inda ake kashe adadi mai yawa a lokaci guda”

“Ya zama dole a bi matakan da suka dace domin kawo karshen wadannan kashe kashen da ake yi a Najeriya musamman jihar Filato” A cewar Obasanjo

 

LEAVE A REPLY