Tsohon Shugaban kasa,Olushegun Obasanjo

Tsohon Shugaban kasa, Olushegun Obasanjo, yana daga cikin mutane 14,771 da ake sa ran zamu karbi takardun girmamawa a bikin yaye dalibai karo na 7 da jami’ar NOUN zata yi nan gaba, a cewar mataimakin Shugaban jami’ar, Abdallah Uba Adamu.

Tsohon Shugaban kasa Obasajo ana sa ran zai kasance daya daga cikin wadan da zasu karbi takardar shaidar kammala karatu a matakin digiri na uku, a fannin Ilimin Nazariyyar addinin Kirista.

Ana sa ran yin bikin yaye daliban jami’ara ranar 20 ga watan Janairun nan mai zuwa a mazaunin jami’ar dake unguwar Jabi a babban birnin tarayya Abuja, tsohon Shugaban kasa Obasanjo na daga cikin wadan da zasu halarci bikin domin mika masa tardun kammalawa.

Haka kuma, Farfesa Abdalah Uba Adamu, yace jami’ar na tunanin daukar Obasanjo a matsayin malami mai kula da dalibai masu neman ilimi mai zurfi. Ana kuma zaton Obasanjon na iya yin aikin koyarwa a jami’ar kasancewar digiri na uku ne matakin da ake daukar malaman jami’ah.

NAN

LEAVE A REPLY