Obasanjo Olushegun

Daga Hassan Y.A. Malik

Tsohon shugaban Nijeriya kuma dattijon kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya yi kira ga ‘yan kabilar Ibo da kar su kuskura su zabi shugaba Muhammadu Buhari a babban zabe mai zuwa na shekarar 2019.

Obasanjon ya bayyana hakan ne a wajen taro gamayyar kungiyoyin Nijeriya da ake kira da Coalition  of Nigeria Movement CNM da aka gudanar a Awka, babban birnin jihar Anambra, inda ya ce ‘yan kabilar Ibo ne za su amfana in har aka kayar da gwamnatin Buhari a shekarar 2019 tare kuma da yi musu alkawarin dan kabilar Ibo ne zai zama shugaban Nijeriya a shekarar 2023.

Obansanjo ya bayyana hakan  ne ta bakin kodinatan CNM na kudu maso gabas, Dakta Okey Nwosu, inda ya yi kira da al’ummar wannan yanki da ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta hana Buhari komawa karagar mulkin Nijeriya a shekarar 2019.

“Wannan taro na yau zaburarwa ne ga al’ummar kabilar Ibo da su hada karfi da karfe da CNM wajen ceto Nijeriya daga yunwa, talauci, mulkin kama karya, nuna kyama ga wata kabila, kashe-kashe daga fulani makiyaya”

“Kowane mai ruwa da tsaki a kasar nan na cike da takaicin yadda ake kai hari ga mutane a cikin garuruwansu, a cikin gidajensu, a kashesu,  a yi musu fyade kana kuma a mayar da su ‘yan gudun hijira a cikin garinsu na gado.

“In har ba a kawo karshen wannan salon mulki ba to lalle Nijeriya za ta iya fadawa cikin wani hali na Lahaula.”

“Babban burin CNM shi ne ganin ta kori Buhari daga fadar gwamnati a 2019 tare da tabbatar da cewa an nada shugabanci nagartacce a Nijeriya,” a sakon na Obasanjo zuwa ga ‘yan kabilar Ibo, wanda Okey Nwosu ya karanta.

LEAVE A REPLY