Tsohon Shugaban kasa Cif Olushegun Obasanjo

Tsohon Shugaban kasar Najeriya, Olushegun Aremu Obasanjo ya isa birnin Monrobiya domin shaida bikin rantsar da sabon zababben Shugaban kasar, George Weah.

Jirgin da yake dauke da tsohon Shugaban kasa Obasanjo ya sauka a birnin Monrobiya da misalin karfe 8:01 na safiyar nan a gogon Najeriya. Za adai a yi wannan bikin rantsar da Weah ne a yau litinin.

Jakadan Najeriya a kasar Mista James Dinka ne ya tarbi sohon Shugaban kasa Obasanjo tare da wakilin musamman na majalisar dinkin duniya a kasar Salihu Uba na daga cikin bakin da suka tarbi Obasanjo.

A lokacin da yake magana da ‘yan jaridu, Olushegun Obasanjo ya bayyana cewar yana alfahari da kasancewarsa a kasar domin shaida wannan muhimmin abin tarihi na mika mulki zuwa ga zababbiyar Gwamnati cikin aminci da salama.

“Ina mai cike da farincikin kasancewata a kasar Laberiya a yau, kuma ina taya ‘yan uwana ‘yan kasar Laberiya murnar wannan muhimmin abin tarihi”

Tsohon dan wasan kwallon kafar kasar, George Weah, zai sha rantsuwar kama aiki a matsayin sabon zababben Shugaban kasar Laberiya a ranar litinin din nan, bayan da ya kayar da mataimakin Shugaban kasar a wani zabe da ya kai zagaye na biyu.

Hukumar zabe ta kasar Laberiya, NEC, ta gabatar da takardun lashe zabe ga sabon zababben Shugaban kasar George Weah da mataimakinsa Jewel Howard-Taylor da kuma sabbin zababbun ‘yan majalisar wakilai ta kasar.

Sabon zababben Shugaban kasar, George Weah, ya bayyana zabensa a matsayin wani al’amari da zai hade kan kasar. Weah zai karbi mulki daga hannu Shugaba Ellen-Johnson Sirleaf.

Sabon zababben Shugaban kasar, ya bayyana cewar zai baiwa dukkan ‘yan kasar cikakken ‘yancinsu kamar yadda dokokin kasar suka tanadar, ba tare da yin wani katsalandan ba.

Shugaban dan shekaru 51 George Tawlon Manneh Oppong Ousman Weah, tsohon kwararren dan wasan kwallon kafar kasar ne, wanda ya buga mata dan wasan gaba.

Tsohon dan wasan kwallon kafar, bayan da ya bugawa kasar ta Laberiya kwallo, ya kuma yi wasan Kwallo a kasashen Italiya da Faransa da kuma Burtaniya, inda ya shafe shekaru 14 a kasashen Turai yana taka leda.

George Weah ya kafa jam’iyyar CDC, inda yayi mata takarar Shugaban kasa a zaben 2005, wanda ya sha kaye a hannun Ellen Johnson Sirleaf a zagaye na biyu.

A zaben da aka kuma gudanarwa a shekarar 2011 a kasar, Weah ya zama dan takarar mataimakin Shugaban kasa,inda yayi takara tare da Winston Tubman a matsayin dan takara, inda daga baya aka zabe shi a matsayin dan majalisar Dattawan kasar a shekarar 2014.

Mista Weah, an zabe shi a matsayin zababben Shugabann kasar Laberiya a shekarar 2017 bayan da ya kayar da mataimakin SHugaban kasa mai ci Joseph Boakai a zagaye na biyu.

LEAVE A REPLY