Daga Hassan Y.A. Malik

Hukumar hasashen yanaye-yanaye ta Najeriya NiMet ta yi hasashen samun ruwan sama a jihohin da ke tsakiyar kasar nan a safiyar yau Litinin.

NiMet ta yi hasashen samun ruwa sama da zai zo da tsawa a birnin tarayya Abuja, da wani bangare na Kaduna, Binuwai, Nasarawa, Kogi, Kwara, Filato, Taraba da Yola.

 

Hasashen har ila yau ya bayyana cewa za a sake samun ruwan da ranar yau a jihohin Filato, Kaduna da Nasarawa.

Hukumar ta NiMet, a hasashenta na jiya Lahadi ta ce yankin kudancin Nijeriya za samu ruwa sama a yammaci zuwa daren yau Litinin.

 

LEAVE A REPLY