Tsohon Gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa kuma mai neman takarar Shugaban kasa karkashin inuwar jam’iyyar PDP, a ranar Juma’a a birnin Kano ya bayyana cewar yana da cikakken ingancin da yasa ‘yan Najeriya zasu watsar da Buhari su zabe shi a zabe mai zuwa. Ya Kara da cewar, shi kadai je dantakarar da Buhari yake mugun shakkar karawa da shi.

Bafarawa ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da shugabannin jam’iyyar PDP na jihar Kano domin neman goyon bayansu a zaben dan takarar Shugaban masa da za a yi na jam’iyyar PDP nan gaba kadan.

Ya kara da cewar idan har za a duba cancanta be wajen yin wannan zabe to ba shakka zai kayar da duk wani dantakarar Shugaban kasa a PDP a zaben fidda gwani na jam’iyyar da za ai nan gaba.

“Ni ne kadai dan takarar Shugaban kasar da yake tayarwa da Shugaba Buhari da sauran ‘yan takarkaru hankali. Domin nayi imani matukar aka kalli abinda nayi a baya da irin nasarorin da na cimma a rayuwa to tabbas ba zarce sa’a “ A cewar Bafarawa.

Sai dai kuma, Shugaban tsagin jam’iyyar PDP na jihar Kano Sanata Mas’udu El-Jibrin Doguwa ya bayyana cewar duk da fama da rikici da jam’iyyar take yi a jihar, babban burinmu shi je samun nasarar zaben 2019.

Daga nan ya roki Attahiru Bafarawa da ya sanya baki wajen ganin an samo bakin zaren warware rikicin da ake fama da shi a cikin jam’iyyar a jihar Kano.

 

 

LEAVE A REPLY