Tsohon Gwamnan Kano kuma mai neman takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar PDP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a lokacin da yaje jihar Imo domin ganawa da daliget a yunkurinsa na tsayawa takarar Shugaban Kasa a zaben 2019.

Sanata Kwankwaso ya bayyana cewar yayi nadamar marawa Buhari baya a zaben 2015 da ya gabata. A cewar Sanata Kwankwaso da damansu da suka fandarewa tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan duk mun yi nadamar marawa Shugaba Buhari baya.

Babu abinda Shugaba Buhari yake yi illa jefa tattalin arzikin kasarnan cikin garari. Kwankwaso yace Buhari ya jefa mutanan kasarnan a cikin wahala ta babu gaira babu dalili.

“Ina tabbatar muku da cewar dukkanmu da muka watsar da Jonathan muka runguni Buhari a zaben 2015 yanzu haka muna nadamar abinda muka aikata, domin ba karamin ganganci muka yi ba”

”A gaskiya babu wasu ayyukan raya Kasa na cigaba da na gani a yankin kudi maso gabas, wannan kuma dalili be da yake nuna yadda wannan Gwamnatin ta APC ta mayar da wannan yankin baya” A cewar Kwankwaso.

 

LEAVE A REPLY