Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Firaministar Burtaniya Theresa May sun amince da kulla yarjejeniyar tsaro da ta kasuwanci tsakaninsu.

Wannan sabuwar yarjejeniya da aka kulla zata baiwa kasashen Najeriya da Burtaniya damar cin gajiyar abubuwan da suka shafi tsaro da cinikayya musamman a wannan mawuyacin lokaci da Najeriya ke fuskantar kalubalen tsaro.

Najeriya dai na bukatar kulla cinikayyar makamai a wannan lokaci da Najeriya take Yaki da ‘yan kungiyar mayakan Boko Haram a yankin Arewa maso gabas da kuma kalubalen barayi da masu kashe mutane a dajin Zamfara da jihar Kaduna.

LEAVE A REPLY