Ana hasashen za’a samu karuwar mutane miliyan 189 a najeriya daga nan zuwa shekara ta 2050 a cewar kwamitin majalisar dinkin duniya dake kula da sha’anin tattalin arziki da walwala da kuma kyautattuwarrayuwar al’umma.

Haka kuma, wannan kwamitin ya gano cewar nan da shekara ta 2050 mutane kimanin biliyan 2.5 a duk fadin duniya zasu baro kauyuka su koma birane da zama don samun kyautatatuwa da kuma ingantacciyar rayuwa.

DAILY NIGERIAN ta habarto wannan kwamitin na cewar “Nan da shekara ta 2050 kasar najeriya zata kasance kasa ta uku mafi yawan jama’a a duniya, wanda a halin yanzu Najeriya ita ce kasa ta 7 mafiya yawan mutane, kuma ta daya mafi yawan bakarfata”

“Kasashen Indiya da Chana da kuma Najeriya sune kasashen da zasu shige gaba wajen yawan mutane a duk fadin duniya, sannan kuma zasu bukaci abinci da ruwan sha sama da sauran kasashen duniya daga nan zuwa shekara ta 2050”

 

LEAVE A REPLY