Daga Hassan Y.A. Malik

Hukumar tabbatar da ingancin abinci da magunguna, NAFDAC ta rufe katafaren kamfanonin magunguna uku da ke sarrafa magungunan tari sakamakon zarginsu da taimakawa wajen amfani da magungunan codeine ba bisa ka’ida ba.

Kamfaninnikan da aka rufe sun hada da: Peace Standard Pharmaceutical Limited, Biroj Pharmaceutical Limited da Emzor Pharmaceuticals Industry Limited.

Babban daraktan hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da fitar a jiya Litinin.
Hukumar da taimakon jami’an ‘yan sanda ta gudanar da bincike a ofisoshin kamfaninka da ke jihar Kwara da jihar Legas. Peace Standard na da Biroj na da ofisoshinsu a garin Ilorin, jihar Kwara, inda Emzor kuma ke da ofis a Ajao estate da ke jihar Legas.

Daraktar ta NAFDAC ta ce za a sake bude kamfanonin kawai in har sun baiwa hukumar hadin kai wajen gudanar da bincikenta da ta ke yi kan fitar codeine da yaduwarsa a hannun diloli.

In ba a manta bai dai a ranar Talatar da ta wuce ne ministan lafiya, Farfesa Isaac Adewole ya umarci NAFDAC da ta haramta sarrafa da kuma shigo da codeine a fadin kasar nan.

LEAVE A REPLY