Sanata Shehu Sanni

Sanata mai wakiltaar Kaduna ta tsakiya a zauren majalisar dattawan Najeriya, Shehu Sani ya bayyana yadda ya sanya madaurin wandonsa a madadin sandan majalisa, kuma ‘yan majalisar suka amince da hakan, kafin daga bisani aka kawo wata sandar majalisar ta daban.

Shehu Sani ya bayyana haka ne a shafinsa na facebook jim kadan bayan da aka yi balahira a zauren majalisa, inda wasu ‘yan daba karkashin jagorancin sanatan da aka dakatar Omo-Agegeg suka shigo suka sace sandar majalisar.

Daga bisani an kawo wani sabon sandar, yayin da majalisar ta baiwa ‘yan sanda sa’o’i 24 da su tabbatar sun dawo da sandar da ‘yan daban suka sace.

LEAVE A REPLY