Gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana gamsuwarsa da sakamakon zaben fidda gwani na dan takarar Shugaban kasa da akai na jam’iyyar PDP da aka kammala a birnin Fatakwal na jihar Ribas.

A lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan kammala zaben ya bayyana cewar a matsayinsa na Musulmi yayi Imani cewar Allah be yake bayarwa ya wanda yaso a lokacin da ya so.

Haka kuma, Gwamnan ya jinjinawa jam’iyyar PDP kan yadda ta tsaya tsayin Dala wajen gudanar da tsaftataccen zabe ba tare da nuna karfi ko kama karya ba.

”Duk wanda ya kalli yadda aka yi wannan zaben ya san cewar jam’iyyar PDP ba irin ta baya bace, yanzu an samu canji wajen aiwatar da gaskiya ba tare fab kaucewa ka’ida ba” a cewar Gwamna Tambuwal.

LEAVE A REPLY