Wasu mahara da akke kyautata zaton Fulani ne sun kai wani hari a kauyen Kikon dake karamar hukumar Numan a jihar Adamawa inda ‘yan kabilar Bachama ke da rinjaye, bayanai sun tabbatar da an kashe mutum 3 tare da jikkata wasu da dama da lalata dukiya.

Rahotanni daga yankin da abin ya faru sun nuna cewar,maharan sun kai harin ne a lokacin da mutanenkauyen suke sharar barci, inda suka dinga harbin kan me uwa da wabi a kauyen.

“Kauyen ya yamutse gaba daya a sakamakon wannan hari, mutane da yawa sun tsere daga  gidanjensu inda wasu suka shiga daji, wasu kuma suka tsallaka garuruwa mkwabta domin gudun ceton rai” A cewar Ngurigon Yohanna, wani da yaci nasarar tsira da ransa.

A daidai lokacin da aka kai harin, cikin gaggawa ‘yan kabilar Bachama suka hada gangamin matasa masu dauke da makamai,inda suka kaddamar da kai wani harin ramuwar gayya a kauyen Dowayan-Waja da kuma Lure inda suka kone komai a garin.

A lokacin da yake tabbatarwa da ‘yan jarida kai wannan harin, Shugabankaramar hukumar Numan Arnold Jibila, ya bayyana cewar, har ya zuwa lokacin basu tabbatar da ko adadin mutum nawa ne suka rasu ba.

Amma sai dai wata majiya ta bayyana cewar, mafiya yawan mutanan kauyen sunyi sansani a cikin daji, domin Fulanin da suka kai harin akalla sun shigo kauyen kan babura guda 20, wasu kuma sun iso da kafa domin kaddamar da kai hari a garin.

Majiyar ta cigaba da cewar, akalla an kashe mutane uku a harin, sannan kuma wadan da suka samu munanan raunuka an dauke su zuwa asibitin garin Numan domin karbar magani.

A lokacin da yake tabbatar da kai hare haren a garuruwan guda biyu, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, Othman Abubakar, yace maza biyu da mata biyu a kauyukan guda biyu ne aka kashe.

Kakakin ya ciga ada cewar, tuni aka garzaya da wadan da suka samu raunuka zuwa asibitin kwararru a Numan domin samun kulawa ta gaggawa.

Ya cigaba da cewar, gidaje da yawa ne aka cinna musu wuta, sannan an barnatar da dukiya mai yawa a garin Kikon da kuma Dowaya-Waja.

Tuni dai rundunar ‘yan sandan jihar ta tura jami’anta zuwa yankin da abin ya faru domin dawo da doka da oda a garuruwan guda biyu.

LEAVE A REPLY