Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo

Daga Hassan Y.A. Malik

Matamakin shugaban Nijeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, a jiya Talata ya bayyyana sunayen mutane uku da suka saci kudi daga baitul malin Nijeriya da adadinsa ya kai Dalar Amurka biliyan 3 (daidai da Nairar Nijeriya tiriliyan 1.08) a zamanin mulkin Goodluck Jonathan.

Osinbajo ya bayyana hakan ne a wajen wani taro da wata kungiya ta ‘yan addinin Kirista ta shirya da ta yi wa lakabi da ‘Get Involved’

Osinbajo ya ci gaba da cewa: “Cin hanci da rashiwa shi ne ya zama babbar barazana ga ci gaban tattalin arzikin Nijeriya. Ga misali: A shekarar 2013, ‘yan kasar nan mutum 3 kacal sun wawushe wasu kudade da ake ajiyewa don biyan ‘yan kwangila kudin fara aiki da adadinsa ya kai dalar Amurka biliyan 3.

“A yau, dalar Amurka biliyan 3 daidai ya ke da tiriliyan 1 na Nairar Nijeriya a daidai lokacin da kasafin kudinmu gaba daya bai shige Naira tiriliyan 7 ba. To, ta ya ya ma za a yi a ce tattalin arzikin Nijeriya ba zai samu tangarda ba?

“A wancan lokacin da ake sayar da gangar man fetur dalar Amurka 100 zuwa 113, sai waccan gwamnatin ta warewa ma’aiakatar sufuri Naira biliyan 15 kacal, ma’aikatar noma Naira biliyan 14. Gaba dayaa ma’aiakatun aka ware musu Naira biliyan 139. A yau farashin gangar danyen man fetur na tsakaniin dalar Amurka 60 zuwa 70, amma mun warewa ma’aiakatar ayyuka, wutar lantarki da gidaje Naira biliyan 450, ma’aikatar sufuri ta samu Naira biliyan 80, ma’aiakatr noma, Naira biliyan 65..kafatanin ma’aikatun sun samu Naira biliyan 560.

“Ta ya ya za ka iya aiwatar da da yawa alhalin kana samun kadan? Ta ya ya muka iya fitar da manya ayyuka da kadan din da muke samu? Ta ya ya za mu iya samar da layin dogo daga Kano zuwa Legas, cibiyar samar da wutar lantarki ta Mambila, gadar Neja ta 2 duk da karancin abinda muke samu? Gaskiyar magana ita ce, da zarar ka takawa cin hanci da rashawa burki, to, fa, za ka iya aiwatar da ayyuka da dama da kudin shiga dan kadan,” inji Osinbajo

LEAVE A REPLY