Shugaban jibiyar Alfurqan kuma babban limamin Juma'aa na Masallacin Alfurqan Kano, Dr. Bashir Aliyu Umar

An yi kira ga ma’aikatan lafiya da suke halin yajin aiki da su ji tsoron Allah su janye yajin aikinsu alfarmar watan Ramadan.

Sheikh Dr. Bashir Aliyu Umar babban limamin masallacin Juma’a na cibiyar Alfurqan ne ya bayyana haka a lokacin da yake bude fara gabatarda Tafseer na watan Ramadan na shekarar2018 a Masallacin Alfurqan dake Kano.

A lokacin da yake gabatar da Tafseer din, Malamin ya bayyana cewar akalla marasa lafiya shida ne suka rasu a jihar Kano a sakamakon rashin wankin koda da suka kasa samu saboda yajin aikin ma’aikatan lafiya.

Malamin ya ja hankalin hukumomi da kuma kungiyar ma’aikatan lafiya da su dubi maslahar rayuwar al’umma. “Da Shugabanni da su ma’aikatan lafiya sai sun kasance ababen tuhuma a gaban Allah ranar alkiyama”

“Wajibi ne hukuma ta duba bukatun ma’aikatan lafiya domin ganin yadda za a biya musu domin ceton rayuwar al’umma, sannan kuma yayi kira ga ma’aikatan lafiya da su sassauto da bukatunsu domin maslahar rayuwar mutanan da suke bukatar kulawar ma’aikatan lafiya”

LEAVE A REPLY