Wasu mutum shida da ake zargi da aikata fashi da makami da kuma yin garkuwa  da mutane a hanyar Kaliyawa zuwa Mahuta a jihar katsina sun shiga hannu, bayan da aka yi batakashi tsakaninsu da jami’an ‘yan sandan jihar Katsina.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina DSP Gambo Isah ya tabbatar da cewar, da misalin 05:00 bayan da aka tseguntawa rundunar ‘yan sandan jihar, suka tasarwa ‘yan fashin a hanyar Kaliyawa, inda suka ci nasarar kama ‘yan fashin.

Ya kuma kara da cewar, an ci nasarar samun bindiga samfurin AK47 guda daya tare da albarushi guda 19 da sauran kayan aikata ta’addanci a tare da ‘yan fashin.

Mutanan da aka kama su ne, Muntari Jibrin 25 da Dabo Hassan 60 da Abdullahi Alhaji Samu 20 da Tukur Mamman 20 da Babangida Sa’idu 27 da kuma Isyaka Yusuf 20.

Kakakin rundunar yace, mutanan sun amsa laifin cewar sune suke yin fashi da makami da kuma yin garkuwa da mutane a hanyar Katsina zuwa Zaria zuwa Funtuwa da yankin karamar hukumar Sabuwa da Dandume duk a jihar Katsina.

Yace ana cigaba da gudanar da bincike kan mutana, inda daga zarar bincike ya kammala za’a mika su gaban kuliya domin su fuskanci Shari’ah.

LEAVE A REPLY