Daga Hassan Y.A. Malik

Sama da ‘yan jam’iyyar APC dubu 20 ne suka sauya sheka suka koma PDP a karshen makon nan a jihar Akwa Ibom.

Masu sauya shekar da daraktan yakin neman zaben jam’iyyar APC a jihar Akwa Ibom a shekarar 2015, Cif Sunny Udom ya jagoranta sun koka akan yadda APC ta dada rikita kasar nan tare da yin alwashin zabar jam’iyyar PDP a zaben 2019.

An karbi masu sauya shekar ne a wajen wata walima da matasan yankin tsohuwar Abak da ke dauke da kananan hukumomi 5 suka shiryawa gwamnan jihar, Gwamna Udom Emmanuel da mai dakinsa Martha don karramasu.

A yayin jawabinsa, Cif Sunny Udom ya bayyana cewa, “Ni da jama’ata mun yanke hukuncin mu bar jam’iyyar APC mu dawo jam’iyyar PDP sakamakon amincewa da muka sauya sheka daga PDP zuwa APC tamkar barin kaskon suya ne ka fada cikin wuta. A saboda haka mun zabi mu dawo cikin kaskon suyar.”

Daga cikin wadanda suka sauya shekar akwai shugaban karamar hukumar Abak, Okon Obot, tsohon dan majalisar tarayya, Cif Nkereuwem Dan, wasu tsofaffin shugabannin kananan hukumomi da kodinatocin mazabu na jam’iyyar APC.

Gwamna Emmanuel Udom ya yabawa al’ummar tsohuwar Abak bisa karrama shu da suka yi tare kuma da yi musu alkawarin ci gaba da gudanar da abubuwan da za su ciyar da kasar gaba.

LEAVE A REPLY