Daga Hassan Y.A. Malik

Hadimi ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai, Malam Sha’aban Ibrahim Sharada, ya jika hantar ‘yan mazabarsa ta cikin birnin Kano da tallafin kayan masarufi da suka hada da kayan abinci da suturu  a karshen makon da ya gabata.

Sha’aban din da a yanzu haka ke neman takarar zama dan majalisar tarayya mai wakiltar birnin Kano (Kano Municipal), ya yi wannan kabakin aziki ne a ranar Juma’ar da ta gabata a ofishinsa na takara da ke a Sharada kwanar Freedom da ke Kano.

Kimanin mutane 3,000 ne suka rabauta da buhuhhuna shinkafa daga Sha’aban Sharada a matsayin tallafin azumi, inda wasu mutum sama da 2,500 suka samu turamen atamfofi.

LEAVE A REPLY