Masu sayar da naman Alade sun bayyana irin garabasar da suke samu na kasuwancin naman Alade a jihar Enugu, kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito.

Wasu daga cikin mahautan da suke kasuwancin naman Alade sun bayyanawa wakilin  NAN dake Enugu,  suka ce sun baar sana’o’in da suke yi a baya suka koma sayar da naman Alade baya bukatar wani jari mai karfi.

Mista Chima Uba, wani mahauci mai sayar da naman Alade a mahadar Amokwe dake kan titin Agbani ya bayyana cewar kasuwancin naman Alade baya bukatar wani jari mai karfi.

“Ina samun riba gwaggwaba sosai a wannan kasuwancin”

“Fara kasuwancin naman Alade baya bukatar wasu kudade masu yawa domin farawa. Akalla kana bukatar Naira 35,000 domin fara wannan kasuwancin naman Alade”

“Abin da kawai zaka bukata domin fara wannan kasuwanci shi ne waje mai kyau, wato fuskar kasuwa, daga sai ka mallaki babban tebur da wuka mai kaifi da idan ka sayar da naman zaka samu akalla ribar Naira 8,000 ko 10,000″ A cewarsa.

Haka kuma, akan titin Amaechi, Mista Ndubisi Agu ya bar sana’arsa ta sayar da kayan gwanjo, ya koma saida naman Alade, kuma yana samun riba mai gwabi.”

“Dan uwana, wanda yake fara sana’ar sayarda naman Alade a watan Augustan shekarar 2016, ya mallaki baburin Adaidaita Sahu da wannan sana’ar sayar da naman Alade, a sabida haka na yanke shawarin barin sana’ar gwanjo da nake yi na koma sayarda naman Alade nima”

“Ina yanka Alade guda biyu a kowacce rana, kuma kwastomomina suna saye wannan naman baki daya a kowacce rana, sannan ina gasawa musamman akan hanyar Enugu zuwa fatakwal nan ma matafiya suna saye suna ci sosai”

Aagu ya cigaba da cewar, a yawancin lokaci yana sayen Alade daga masu kiwonsa ne.

“A wasu lokutan nakan sayi lafiyayyen Alade daga 22,000 zuwa 30,000 da wannan kudin zaka samu Alade bul bul”

“Kilo daya na naman Alade mukan sayar da shi akan Naira 1,200, bayan haka kuma, mukan yanka na yadda kwastoma yake son ya saya”

Mista ikenna Ohire ya shaidawa NAN cewar yana fara kasuwancin sayar da naman Alade tun daga karfe 9 na safe har zuwa 11 naman ya kare.

Ohire ya kara da cewar, a wani zubin mukan sayar da Kilo daga 1000 zuwa naira 1,200.

Haka kuma, masu kiwon Aladen su shaidawa kamfanin dillancin labarai na najeriya NAN cewar harkar kiwon Alade tana bunkasa kwarai a jihar Enugu sabida garabar da mutane suke kwasa ta naman Aladen.

Wani ma’aikacin gwamnati, Mista Anthony Egwu, wanda yake makiyayin Alade ne a Umuchi Igbo-Nike ya bayyana cewar, kiwon Alade yana da sirrin da yawan mutane basu gano ba, kuma yana da riba sosai, wanda ya kamata duk wani mai san samun riba ya shiga wannan harkar.

“A matsayina na ma’aikacin Gwamnati, tias nake harkar kiwon Aladai domin bunkasa hanyar samun kudina, musamman a wannan lokacin da na kusa yin ritaya”

“Farashin kowanne Alade ya danganta da yanayin girmansa. Idan ya rika ya zama kato mukan sayar da shi akan Naira 55,000 idan kanana ne ko matsakaita mukan sayar da su akan naira 20,000 ko 25,000″ A cewarsa.

Wata mata da itama take kiwata kananan Aladai mai suna Blessing Uduma a wani gari dake bayan babban birnin Enugu mai suna Akwuke, tace bukatar mutane ta naman Alade na karuwa sosai”

Blessing Uduma ta bayyanawa NAN cewar takan sayar da Alade biyar zuwa shida a kowacce rana.

“Masu sayar da naman Alade a ko da yaushe suna tuntubata, Nakan sayar da Alade har byar a rana musamman idan ina da matasa sosai da na kiwata” A cewarta.

A lokacin da yake tattaunawa da NAN wani mai sayen naman Alade Madam Esther Odukwe ta bayyana cewar naman Alade na gara lafiyar jiki sosai”

Tace kuma, Alade ba shida tsada sosai ba kamar Kaji da naman Shanu ba.

Hakakuma, wani mai sayen naman Aladen shima Madu Edwin bayan kasancewar naman Alade mai arha sosai kuma yana kara lafiyar jiki.

NAN

LEAVE A REPLY