Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje

Gwamnan jihar kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewar yana maraba lale da zuwan tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a yunkurin tsohon Gwamnan na kawo ziyara jihar Kano a karshen watan nan.

Tsakanin Gwamna Ganduje da tsohon Gwamna Kwankwaso ta yi tsami tun farkon Gwamnatin Ganduje.

Tuni dai rahotanni suka tabbatar da cewar, tsohon Gwamnan Kano wanda Sanata ne a yanzu Alh. Rabiu Musa Kwankwaso yana shirin kawo ziyara jihar Kano daga Abuja babban birnin tarayya a ranar 31 ga watan Janairu.

Batun wannan ziyara ta tsohon Gwamna Kwankwaso da zai kawo jihar Kano na daga cikin abinda ake yawan tattaunawa a jihar kano. Da yawa na bayyana tsoronsu ga wannan ziyara, sabi a cewar da dama ziyarar na iya haifar da rigima tsakanin magoya bayan Kwankwaso na kuma na Gwamna me ci Ganduje.

A cewar Kakakin Gwamnatin Kano kuma kwamishinan yada labarai Muhammad Garba, yace, Gwamnatin Kano na maraba lale da Sanata Kwankwaso, yace a shirye Gwamnati take ta yi masa tarba ta musamman, domin Kano na yiwa kowane irin bako barka da zuwa.

A lokacin da yake bayyana irin Nasaririn da Gwamnatin Ganduje ta samu, Kwamishinan wanda ya kira taron manema labarai a ranar talata, ya bayyana cewar, an san jihar Kano da karrama bako, dan haka zasu yi duk abinda ya dace don karrama bakonsu Kwankwaso.

Kwamishinana ya kara da cewar, Gwamnati ba zata taba hana wani dan siyasa bayyana ra’ayinsa a jihar Kano ba, matukar zai kiyaye bin doka da ka’ida.

“Wannan Gwamnati ta Mai Girma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, an santa da karrama tare da mutunta baki a koda yaushe suka yi nufin kawo ziyara jihar Kano, kowa na da masaniyar yadda Gwamna yake mutunta bakin jihar Kano a ko yaushe, to haka ma Sanata Kwankwaso, muna masa marhabin”

“Muna yiwa Kwankwaso barka da zuwa idan zai zo Kano, muna fatan ya zo yayi duk harkokin sa na siyasa, abinda kawai ba zamu lamunta ba shi ne, tashin hankali da hatsaniya, matukar za’a tayar da hankalin al’umma ba zamu taba kyale mutum ba ko waye shi”

Haka kuma, Kwamishinan ya jaddada aniyar Gwamnatin Ganduje na kammala dukkan ayyukan da ta gada daga tsohuwar gwamnatin Kwankwaso.

LEAVE A REPLY