Wani mummunan hadarin mota yaci mutane 15 a jihar Ogun dake kudu maso yammacin Najeriya daga ranar 11 gga watan Yuni zuwa 20 ga wata.

Babatunde Akinbiyi kakakin rundunar hukumar kiyaye aukuwar hadurra ta kasa reshen jihar Ogun ne ya bayyana hakan a wata zantawa da yayi da kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, a birnin Abeokuta a ranar Asabar.

Kakakin hukumar ya bayyana cewar galibin wadannan hadurra sun auku ne a yayin bukukuwan Sallar Eid kara da ya gudana a duk fadin Najeriya.

Ya kara da cewar an samu taho mu gama sau goma sha biyu da ya kunshi motoci na gida guda shida da kuma motar haya guda hudu da babbar motar diban mutane ta gida guda uku da kuma kananan motocin haya guda bakwai da kuma babura guda biyu.

“a yayin wadannan hadura da suka auku, ya rusta da mutane 142 inda a cikinsu mutane 53 da suka kunshi maza 31 da mata 22 suka samu munanan raunuka”

“Yayin da mutane 15 da suka hada da maza 7 da kuma mata 8 suka rasa rayukansu, an kuma ci nasarar kubutar da mutane 74 ba tare da sun ji ko kwarzane ba, yayin da hukumar ta samu kira sau 15 domin bayar da agajin gaggawa” A cewar  kakakin hukumar.

LEAVE A REPLY