Mukaddashin SHugaban kasa Yemi Osinbajo

Mukaddashin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bayar da umarnin sake fasalta rundunardake yaki da ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane, wadda aka fi sani da sunan SARS.

Wannan umarni ya fito daga mukaddashin Shugaban kasa bayan da akai ta samun korafe korafe da rahotanni kan ayyuka na cin zarafi da SARS suke yiwa jama’a.

Ana dai zargin jami’an SARS da keta alfarma jama’a da kuma cin zarafin dan adam.

A saboda haka ne, mukaddashin Shugaban kasa Osinbajo ya umarci Sifeto janar na rundunar ‘yan sandan Najeriya, ba tare da wani bata lokaci ba da yayi garambawul akan ayyukan SARS din.

 

LEAVE A REPLY