Daga Hassan Y.A. Malik

Magidanci mai shekaru 35 da haihuwa, Bawa Joshua ya gurfana a gaban kuliya a kotun majistare da ke Ado-Ekiti a jiya Litinin sakamakon zarginsa da antayawa mai dakinsa Grace tuwon Semovita a lokacin fda ya ke silala.

Maoi shigar da kara, Johnson Okunade ya fadawa kotu cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne a ranar 7 ga watan Mayu, 2018 da misalin karfe 8:00 na darea a kan titin Ayoomodara cikin garin Ado-Ekiti.

Johnson Okunade ya ci gaba da cewa, cacar baki ce ta kaure tsakanin ma’auaratan inda nan take mijin ya dauki tukunyar tuwon ya juye akan matarsa, dalilin da ya haddasa mata rauni a jikinta.

Mai shigar da karar ya ci gaba da cewa, laifin ya sabawa kundin laifuka sashe na 415 na kundin laifuka na shekarar 2012 na jihar Ekiti.

Mai shigar da karar ya nemi kotu da ta dage sauraron karar don ya gabatar mata da shaidu

Lauyan wanda a ke kara, Kayode Oyeyemi ya roki kotu da ta bayar da belin wanda ya ke karewa tare da tabbatarwa da kotu cewa zai gabatar da wanda ake karar a zaman kotu na gaba.

Mai shari’a Adesoji Adegboye ya bada belin Bawa Joshua akan kudi N50,000 tare da dage sauraren karar zuwa ranar 15 ga watan Yuni, 2018.

LEAVE A REPLY