Sanata Dino Melaye

Sifeto janar na rundunar ‘yan sanda ta kasa, Ibrahim Idris, a karo na biyu ya kuma kin amsa gayyatar majalisar dattawa a yau.

Tun da farko an yi tsammanin Sifeton zai yiwa majalisar dattawa bayanin yadda aka yi aka haihu a ragaye dangane da batun kokarin kama Sanata Dino Melaye, dan majalisar dattawa mai wakiltar jihar Kogi ta yamma a majalisar dattawan Najeriya.

A satin da ya gabata ne, majalisar ta cimma amincewa kan a gayyato Sifeton janar na rundunar ‘yan sanda ta kasa, domin ya zo zauren majalisar yayi bayanin abubuwa da suke faruwa na kashe kashe a Najeriya da kuma batun kama Sanata Dino Melaye.

Haka kuma, a wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kasa ta bayar, ta bayyana cewar, Sifeton ‘yan sandan na kasa ya tafi yankin Birnin-Gwari a jihar Kaduna domin duba yadda halin tabarbarewartsaro yake a yankin.

Sanarwar ta cigaba da cewar, Sifeton ‘yan sanda na kasa Ibrahim Idris tare da Shugaban rundunar ‘yan sanda ta kasa shiyya ta daya reshen jihar Kaduna Mohammed Mohammed sun tafi Birnin-Gwari domin duba halin tsaro a yankin.

LEAVE A REPLY