Daga Hassan Y.A. Malik

Wani matashi dan shekaru 25 a garin Ilorin ya kashe kansa ta hanyar rataya bayan da kungiyar AS Roma ta lallasa FC Barcelona a wasan cin kofin zakarun turai a wasa na kusa da na kusa da na karshe a makon da ya gabata.

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Kwara ta tabbatarwa manema labarai da faruwar hakan a birnin Ilorin.

Matashin ya kashe kansa ne ta hanyar rataya bayan ya rataya kansa a cikin dakinsa.

An samu labarin cewa ya fadi a cacar da ya saka ne a wasan kwallon kafan a tsakanin kungiyar kwallon kafan FC Barcelon da AS Roma.

Abun ya faru ne a yankin Oko-Erin da ke birnin Ilorin.

Matashin ya shiga cacar da kudirin cewa FC Barcelona za ta lallasa AS Roma a wasan su na karo na biyu a filin kwallon kafan Nou Camp.

Duk da haka, bayan an buga wasan AC Roma ta lallasa FC Barcelona 0-3 wanda hakan ya ba ta damar kasa Barcelona.

Sakamakon wasan da aka buga ya sanya mamacin ya rasa babur na sa wanda ya saka a caca.

Hakan ya sa matashin ya shiga cikin wani hali musamman don ya rasa babur na sa wanda da shi ya ke samun na cin abinci..

An gano cewa saboda matashin ya rasa yadda zai yi da rayuwansa, shi ya sa ya yanke hukuncin kashe kasan ta hanyar rataya.

Kakakin rundunar ‘yan sanda reshen jihar Kwara, Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da kisan kan da matashin ya yiwa kansa.

Okasanmi ya ce an gano cewa mamacin ya kashe kansa ne sakamakon yawan bashin da mutane ke binsa, inda ya ce “mutane da dama na bin matashin bashi.”

LEAVE A REPLY