Daga Hassan Y.A. Malik

Matasan yankin Neja Delta guda 90 ne suka samu tallafin kudi na Naira dubu 500 kowannensu domin fara sana’o’i, bayan da suka kammala wata horaswa a kan harkokin noma da wasu sana’o’i masu alaka da ita.

Ma’aikatar harkokin Neja Delta ce ta shirya shirin domin baiwa matasa damar fara sana’o’in cin gashin kansu.

Ministan harkokin Niger Delta, Usani Usani ya yi kira ga wadanda suka ci moriyar shirin da su yi amfani da kudaden a abunda ya dace ba a shiririta ba.

Ya kuma shawarci mata da matsan yankin da su yi amfani da damarmakin da gwamnatin tarayya ta samar  masu na inganta rayuwar su.

Usani ya ce ma’aikatar ta jajirce wajen baiwa mata da matasa tallafin da zai rage talauci da yunwa da mutanen yankin ke fama da ita.

LEAVE A REPLY