Wasu matasa sun ci nasarar dakile yunkurin wata ‘yar kunar bakin wake da ta yi nufin tayar da bom din da yake jikinta a wani masallaci a kauyen Gashua a yankin karamar hukumar Gujba a jihar Yobe.

Matasan dai sun ci nasarar dakile harin da matar yta so kaiwa masallacin ne a lokacin da suka mike domin tayar da Sallah, sai wasu suka hangi matar na yunkurin tayar da bom din dake jikinta, cikin gaggawa suka tasar mata kuma suka ci nasarar dakile yunkurinkai harin da matar ta yi.

Tuni matasan suka mika matar ga jami’an rundunar Zaman Lafiya Dole dake yankin. Jami’an sun kuma ci nasarar kwance bom din da aka danawa matar ba tare da ya tashi ba, inda suka raba ta da bom din dake layyace a jikinta.

Ko a ranar Juma’a da ta gabata, an ci nasarar dakile wani harin kunar bakin wake da wasu mata suka yi yunkurin kaiwa a kauyen Kawuri dake yankin karamar hukumar Kunduga.

LEAVE A REPLY